Mu ‘Yanfaila ne
Almajiran Shehu Ibrahim Inyass Kaulakha (RTA)
Farkon abin da muka riƙe La ilaha illallahu
Sannan KaÉ—aita Fuska ga Allah
Dauwama Cikin Zikirin Allah
Karatun Ƙur’ani
Salati ga Manzon Allah (SAW)
Tsarkake Aiki don Allah
Soyayyar Waliyyan Allah
Ɗaukar Cutar Halitta da Yin Haƙuri
Kyawawan Ɗabi’u tare da Bayin Allah
Kyakkyawan Zato ga Allah
Ganin Baiwar Allah
Fauwala Lamari ga Allah
Yin Aiki Ko Yin Sururi don Amfanin Kai da Iyali
Bin Horon Allah da Nesanta da Hane-hanen Allah